Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Wa Wadanda Suka Fice Daga APC Fatan Alheri.
Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada manufar mulkin sa wajen bin tafarkin dimokradiyya, bayar da ‘yanci da kuma barin kowa ya bi zabin da ran sa ke so.
Sannan kuma ya nanata cewa zai yi aiki tare da dukkan Mambobin Majalisar Tarayya da na Majalisar Dattawa.
Da ya ke magana bayan wasu Mambobin Tarayya da na Majalisar Dattawa sun fice daga APC zuwa PDP, Buhari ya kara da cewa dadin da ya ji shi ne, daga cikin dukkan wadanda suka fice din, babu wanda ke kullace da shi ko ya ke fushi da shi.
Shugaban ya ce shi ma bai kullaci ko daya daga cikin su ba. Don haka ba ya fushi da kowanen su.
No comments:
Post a Comment