Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Tuesday, 24 July 2018

Kwankwaso Da Sanatoci 14 Sun Canza Sheka Da APC zuwa PDP

 Kwankwaso Da Sanatoci 14 Sun Canza Sheka Da APC zuwa PDP.


Image result for Kwankwaso da sanatoci 14 sun


Akalla yan majalisar dattawa 14 suka sauya sheka daga jam'iya mai mulki ta APC zuwa PDP cikin su a kwai tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
.
Sanatocin sun bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da suka sa hannu kana suka mika ma shugaban majalisar ya karanta
.
Saraki ya karata wasikar a gaban sauran yan majalisar a zaman da suka yi ranar talata 24 ga watan Yuli
.
Ga sunayen wadan suka sauya sheka kamar haka:
.
Rabui Musa Kwankwaso (Kano)
.
Sanata Barnabas Gemade (Benuwe)
.
Sanata Dino Melaye (Kogi)
.
Sanata Isa Hamman Misau (Bauchi)
.
Sanata Lanre Tajouso (Ogun)
.
Sanata Shaaba Lafiagi (Kwara)
.
Sanata Mohammed Shittu (Jigawa)
.
Sanata Ubali Shittu
.
Sanata Rafiu Ibrahim (Kwara)
.
Sanata Suleiman Hunkuyi (Kaduna)
.
Sanata Monsurat Sunmonu (Oyo)
.
Sanata Ibrahim Danbaba (Sakkwato)
.
Sanata Usman Nafada (Gombe)
.
Sanata Suleiman Nazif (Jihar bauchi)
.
Sanata Abdul'azeez Murtala Nyako (jihar Adamawa)
.
Bisa ga wannan sabon canji da aka samu jam'iyar PDP ita ce jam'iya mafi rinjaye a zauren majalisar dattawa
.
Shugaban majalisar ya bayyana bacin ran sa game da lamarin da ya faru a gidansa inda jami'an tsaro suka tare hanyoyin shiga
.
Yace "kowa nada yancin shiga akida da yake so. Ina nan har sama da sanatoci 15 sun sauya sheka zuwa wata jam'iya amma ba'a yi ma gidajen su
.
Jami'an sun tare duka hanyoyin shiga layin gidansa dake unguwar Maitama nan garin Abuja safiyar ranar talata 24 ga wata
.
Kamar yadda hadimin sa ya sanar yan sandan sun tare shi ne yayin tafiya shelkwatar rundunar gomin amsa gayyatar da sufeton yan sanda ya tura masa kan batun barayin garin Offa.

No comments:

Post a Comment

Pages