Jaruma Zainab Indomie ta Farka domin cigaba daga inda ta tsaya a KannyWood.
.
.
An daina jin duriyar ta a dandalin nishadantarwa na tsawon lokaci bisa ga wasu dalilai
.
.
Bayanai da suka fito daga jarumi Adam Zango sun nuna cewar Indomie ta shirya domin fafatawa a masana’antar kamar waccan lokaci kafin ta taka burki
.
.
Jarumin ya mamaye shafi sa na dandalin sadarwa da hotunan domin nuna farin cikin sa bisa biyayar da take nuna masa
.
.
Jarumar tana daya daga cikin jarumai mata dake kan gaba da farfajiyar kamfanin White house family wanda Adam Zango ke jagoranta
.
.
Zainab Indomie tana daya daga fitattun matan kannywood da suka raya masana'antar gabanin fitowar sabbin fuskoki da ake damawa dasu yanzu
.
.
Tuni dai jarumar ta sanar da dawowar ta dandalin fim kuma daga bisani ta far fitowa a wasu wasanni da ake shiryawa a halin yanzu
.
.
A bikin karamar sallah da ya gabata jarumar ta fito tare da uban gidan ta Adam Zango domin nishadantar da jama'a a wani wasa da aka shirya a jihar Kano.
No comments:
Post a Comment