Ba Zan Amsa Gayyatar Rundunar `Yan sanda Ba — Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya kalubalanci Shugaban Rundunar ‘yan sanda kan ya turo jami’ansa su yi masa tambayoyi a maimakon ya amsa gayyatar da rundunar ‘yan sandan ta yi masa kan zarginsa da hannu kan wani fashi da makami da aka yi garin Offa a jihar Kwara inda mutane 31 suka mutu.
Saraki ya nuna cewa yana da masaniya kan cewa Shugaba Buhari ya umarci Shugaban ‘yan sandan kan su samu matsayinsa kan Fashi da makamin a rubuce ko kuma jami’an ‘yan sandan su same shi kai tsaye don neman karin bayani a maimakon gayyatarsa.
No comments:
Post a Comment