Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Saturday, 26 May 2018

Wata Matashiya ta shigar da Iyayen ta Kotu akan Sun hana ta Auren 'yar uwar ta Mace



A Najeriya wasu iyaye sunyi hannun riga
na har abada da 'yarsu sabida sun gano
tana son ta auri wata 'yar uwarta mace

- Matshiyar da iyayenta suka sallamata ta
garzaya wata kotu inda ta bukaci da mai Shari'a ya daura
mata aure da wata 'yar uwarta mace

- Kotun dau taki amincewa da wannan bukatar haka nan
kuma iyayenta sun sanar a jarida cewa sun
sallamata har abada
Duk da cewa dokokin Najeriya sun
haramta auren jinsi iri daya,
masoya da dama na jinsi iri daya sukan
fito fili su bayyana wa jama'a cewa
suna soyaya sai dai ba kasafai ake
samun wanda suka tunkarar kotu don
daura musu aure ba.

Wannan matashiya mai suna Shalom
Shoremi yar asalin jihar Ogun ta hadu
da fushin iyayenta inda har suka
sallamata ga duniya bayan sun gano ta
tafi wata kotun tarayya inda ta bukaci a
daura mata aure da wata 'yar uwarta mace.

Iyayenta da sauran 'yan uwanta sunyi
Alla wadai da abinda ta aikata har ma sun
sanar da cewa sun sallamata har abada
a shafukan jaridu na kasa.



Wannan matashiya dai ta shigar da karar ne bayan gabatar da kudurin wajen iyayen ta na Son Auren wata 'yar uwar ta mace, a lokacin ne su kuma sukai Tir da wannan Al'amari nata tare da watsar dashi, ita kuma ta shigar da karar ne a wata kotun
Najeriya saboda an hana ta auren 'yar uwarta
mace
Kamar yadda sanarwar jaridar ta
bayyana, kotun ta ki amincewa da
bukatar matashiyar saboda ya ci karo
da dokar hana auren jinsi guda na  2014,
wanda ya yi bayani karara cewa laifi
ne yin auren jinsi a dokar Najeriya.

Dokar kuma ta akwai hukuncin zaman
gidan kaso na shekaru 14 ga wadanda
aka samu suna soyaya tsakanin jinsi iri
daya.

Bayan bayyana cewa sun sallamata ga
duniya, iyayen Shallom sun kara da
cewa sun haramta mata cin gadonsu
har abada.

A wata labarin, NAIJ.com ta ruwaito
cewa Prime Ministan kasar Ingila,
Theresa May ta yi kira ga Najeriya ta
janye dokar hana auren jinsi guda. Ta
kuma mika irin wannan rokon ga
sauran kasashen da Ingila ta raina.

No comments:

Post a Comment

Pages