Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade a wadansu hukumomin gwamnatin kasar a ranar Alhamis.
Wadanan nan nade-nade na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2019, wanda shugaban ke takara domin neman wa'adi na biyu.
A baya dai an soki shugaban da jan-kafa wurin yin nade-nade abin da ya sa wasu 'yan jam'iyyar sa ta APC ke cewa "sun tura mota amma ta budesu da kura".
Ya nada Dokta Anas "Ahmad Sabir" a matsayin babban daraktan asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Dan-Fodio dake Sakkwato.
Sai Dokta "Theresa Obumneme Okoli" wadda ya nada shi sabon shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Horas da Malamai da ke garin Umunze a jihar Anambra.
Akwai kuma Dokta Emmanuel Ikenyiri wanda ya nada shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Horas da Malamai da ke garin Omoku a jihar Rivers.
Har ila yau, Shugaba Buhari ya nada Dokta Pius Olakunle Osunyikanmi a matsayin daraktan wata hukumar ba da agaji wanda ake kira Technical Aid Corps.
A karshe shugaban ya bukaci mutanen da su yi aiki tukuru kuma su kasance masu mutunta dokokin aiki.
Wasu na ganin wadannan nade-naden da shugaban keyi a 'yan kwanakin nan baza su rasa nasaba da kokarin gyara kura-kuran da yayi ba kafin babban zaben na gaba.
No comments:
Post a Comment