Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Thursday, 31 May 2018

Rasuwar Ali Banat Matashi mai Temakon Addinin Musulunci

Ali Banat

Gare ku wadanda baku san shi ba, Jiya Talata Allah (S), ya karbi Ransa bayan kansa ta makura ta kamashi a duk sassan jikinsa (Wadda a turance ake kira da da stage 4 cancer), Cutar dajin da ta wuce misali wacce idan Cutar daji takai wannan matsayin da wuya mutum ya rayu. dama ya kasance matashi mai Arziki kuma mai hidimtawa marasa galihu da dukiyarsa.

Watanni kalilan kafin wannan wata likitoci suka tabbatar masa da Cutarsa tayi nisa don haka da wuya Ya kara Watanni masu yawa anan gaba.

Ali wanda tun kafin a sanarda shi wannan ya mika rayuwarsa da dukiyarrga kacokan ga marasa galihu musamman na wannan yanki namu afrika, inda yakan gina musu gidaje tare da rijiyoyi da sanya 'ya'yan marayu makaranta da sauran ayukkan alkheri.

kuma Ali har ya bar wannan duniya jiya kenan wannan shine aiki da yasa a gaba.


Kafin Mutuwarsa dai ya fitarda wani tsari na taimakawa musulmin da basuda karfi na duk duniya wanda ya sanya masa take, MATW Project (wato Muslims Around The World).

Babu shakka wannan Wa'azine garemu Idan zamu hankalta mu taimakawa marasa galihu domin wata rana bama wannan duniyar kuma abinda mukayi sadaka shi zamu gani a CIKIN QABARI DA GOBE QIYAMA.

Allah yajikan ka Ali kaida dukkan Musulmi.

1 comment:

  1. Enter your comment...may Allah the allmighty forgive him and in-light his grave, insert him in paradise.ameen.

    ReplyDelete

Pages