_59_
Ba tare da yako kallesu ba ya wuce yana yiwa sadiq hira domin yanda suke fushi dashi haka shima yake fushi dasu,
"Mtswwwww" ihsan taja dogon tsaki,
"Ai wallahi sai mun gyara masa zama acikin gidan nan daga shi har wacce yake shirin kawowa gidan" fadila tafada cikin jin haushi,shi dai Lamido bai San suna yi ba tafiyarsa yayi zuwa gidan baffa,
Babu kowa a falon dan haka ya wuce dakin ikhlas tana zaune akan gado cikeda damuwa, "woww!!! Handsome" tafada Acikin mind dinta daidai lokacin da idanuwanta suka hango mata kyakkyawan dressing din da lamido yayi ba karamin kyau yayiba domin yana ji da kyau da gayu, mika mata sadig yayi ya juya zai fita,
"Abban sadiq dan Allah kayi hakuri wallahi ba laifina bane" ya jiyo muryar ikhlas,
Juyowa yayi "shikenan ya wuce amma dan Allah ki rinka kulawa,ki bashi abincinshi yasha idan yagama ina falo ki kawo min shi"
Fita yayi yaje kan dining ya debi abincin da zai ci, zama yayi yaci yasha ruwa ya tashi ya koma falo ya zauna, yana zama ikhlas na fitowa,
Sadiq ta bashi ta juya zata tafi,
"Kinga dan jona min kayan kallon nan pls" yace da ita tareda fara yiwa sadiq wasa, harshen sadiq ya kama yana yi masa wasa shi kuma sadiq din sai dariya yake kyalkyalawa,
Tv ta jona masa ta juya ta koma dakinta ta kwanta, kwanciyarta babu dadewa bacci ya dauketa daga karshe ma bata san lokacin da lamido ya dawo da sadiq ba dan sai wurin 3 ta tashi taga sadiq akusa da ita shima yanata baccin.
Washe gari da azumi ikhlas ta tashi saboda ana binta azumi guda daya bata rama ba,
Akwance ta wuni tana bacci sai da yamma ta fito tana goye da sadiq, innah ta samu a falo ita da lamido suna hira, ai sadiq na ganin lamido ya fara tsalle yana murna kamar zai fado daga bayan ikhlas yanda yake yi kamar zai kunce zanin ya sauko abin har mamaki ya bawa ikhlas saboda ta fahimci sadiq yanzu ya gama gane lamido sosai,
Sauko dashi tayi ta mikawa lamido,
"Saddiqu na ka tashi daga baccin? To zo mu gaisa"
Tana jinshi ya takarkare yana ta yiwa sadiq din wasa, kitchen ta shiga ta fara gyara wake saboda alale take son yi,
Kunun shinkafa ta dama ta fito, iya innah ce kadai a falon da alama lamido ya fita da sadiq,
Kitchen ta sake shiga bayan an markado mata waken, alalanta ta shirya mai dadi wanda yasha alayyahu da dafaffiyar hanta,
Ana kiran salla ta gama, kayan ta diba takai dakinta bayan ta dibarwa innah nata,
Sanyayyen zobon data dama ta diba tasha kawai taje ta dauro alwala bayan tayi wanka saboda tana son taji karfin jikinta,
Doguwar riga marar nauyi mai hannun shimi ta saka tayi salla tana idarwa ta cire hijab dinta tajawo kwanon alalanta ta dauki filet ta saka zata fara ci kenan lamido ya shigo dauke da sadiq a kafadarsa,
Agefen gado ya kwantar dashi ya dawo gabanta ya zauna, flaks din gabanta ya fara bubbudawa yana gani,
"Babu tayi?" Yafada bayan ya langabe kanshi yana kallonta, rigar jikinta ba karamin kyau tayi mata ba, tayi mata caras sannan babu wanda zai ganta yace ta taba haihuwa,
"Bisimillah" ikhlas tace dashi cikin jin kunya, cup ya dauka ya tsiyayi kunun gyada yafara sha tareda tsareta da ido yana karewa surarta kallo,
Duk ikhlas tagama takura gashi takasa sakewa taci abincin da ta ci burin ci, duk yanda takai ga kwadayin alalan nan haka ta kyale tana cakularsa,
"Azumi kikayi?"
"Eh" ta bashi amsa a hankali,
"Azumin me? Ramuwa?"
Girgiza kai tayi alamar a'a,
"Ok ai na dauka ko baki cika ramadan din ba"
Shiru tayi bata cemasa komai ba amma da alama kunun nata yayi masa dadi domin har ya shanye mata rabi, ita dai alla alla take ya gama ya tafi domin ta samu ta sake taci abincinta,idonshi ya zubawa kyakkyawar fuskarta kurrr baya ko kiftawa amma ya lura sam ta kasa sakewa dashi domin abincin ma ta kasa ci saboda yana wurin,
Tashi yayi yai mata sallama ya tafi sai alokacin ta iya cin alalanta.
Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali kullum lamido yana gidan innah manne da sadiq, su kansu su fadila suma yanzu sun sauke abinda yake kansu sun shirya da lamido amma fa ta ciki na ciki,
Ikhlas na zaune adaki tana goge kayanta taji wayar ta na tsuwwa dauka tayi anan yake sanar da ita ta shirya anjima zai zo ya kaita gidan barrister elmustapha, kashe wayar tayi tana cewa "yau ka ga dama kenan zancen da tun sati uku da suka wuce na rinka binka ka kaini kaki"
Tashi tayi ta shirya ta saka atamfa ja da jan mayafi tasaka sarka da dan kunne golden,
Shirya sadiq tayi bayan ta gama shiryawa, blue din wando ta saka masa da pink din riga ta saka masa safa pink da blue din takalmi,
Tana kammala shiryawa lamido na shigowa, sallama taje ta yiwa inna ta fito suka tafi yana rikeda sadiq, ba karamin kyau yaga prettynshi tayi ba gaba daya ta tafi da tunaninsa,
"Yaushe zan zo mu tafi?" Ya tambayeta lokacin da suka karasa kofar gidan elmustspha,
"Sai da daddare" ta bashi amsa,
"No yamma dai"
Langabe kai tayi "dan Allah ka bari sai dare" tace dashi cikin shagwaba,
Mika mata sadiq yayi batare da yace komai ba, nan daddadan kamshin jikinta yakaiwa hancinsa ziyara wanda ya nemi rikitashi,bude kofar motar tayi ta fita ahankali tana dan murmushi wanda ita kanta bata san dalilinta na yinsa ba,kallonta ya rinka yi har ta bacewa ganinsa,sai da yaga shigarta gidan sannan ya tafi.
Tunda sukaje gidan bini bini sai Lamido ya kirata awaya ya tambayeta sadiq da haka har dare yayi sai wurin 8 yazo daukarta,
Perfect suya spot ya nufa dasu wato wurin sayar da kayan makulashe, packing yayi agefen titi ya jiyo yana kallonta,
"Me zan taho miki dashi?"
"Babu komai"
"Baki isaba dole sai kin fada wallahi"
Fuskarshi yakai saitin tata"uhm fadi ina jinki"
"Donote da meat pie ko fish pie.." Tafadi cikin jin kunya,
Kallon tsukakken bakinta yayi yanda take magana"ai wannan bakin Naki shine meat pie da donote din" yace da ita yana kashe mata idonshi daya,
Fita yayi daga cikin motar yabarta da murmushi akan fuskarta,
Tana nan zaune yaje ya dawo hannunshi dauke da ledoji guda 3 iri daya, biyu ya mika baya ya ajiye ita kuma ya ajiye mata daya akusa da ita, ledar tata ya buda ya dauki meat pie guda daya yafara ci yana driving,
Ido ta zuba masa tana kallonsa yayi kyau ainun kasancewar ya sake wanka ya sake shiga cikin yellow din riga da jan wando ga kyakkyawan sajenshi kwance akan fuskarshi sai sheki yake sannan duk taunar da yayi sai kumatunsa ya lotsa,
Ganin tanata kallonsa yasa lamido juyowa ya kalleta, "meye kiketa kallona ne ko baki baniba na baki kayanki?"
Daurewa tayi ta mika masa hannunta tana murmushi "bani kayana.."
Murmushi yayi maimakon ya bata sai ya kama hannunta ya rike cikin nashi,daga shi har ita wani yarrrr! Sukaji sakamakon wani bakon al'amari da ya ziyarcesu lokacin da hannuwansu suka hadu da juna,sunkuyar da kanta tayi tana jin yanda yake matsa yan yatsunta,
Ahankali yake juya hannunta mai mutukar laushi cikin nashi har sukaje gida amma ikhlas ta fuskanci duk kasala ta kamashi domin kamar dakyar yake yin tukin gashi idonshi yadan kad'a ya sake launi, sakin hannunta yayi ta dauki sadiq kasancewar yayi bacci,cikin kasala ya riko mayafinta nan ta jiyo tana kallonshi, matsawa yayi ya mannawa sadiq kiss a goshi,kallonshi ya mayar gareta sai da gabanta ya fadi sakamakon haduwar da kwayar idanuwansu suka yi,cikin azama ta sauke nata idon akasa domin bazata iya cigaba da kallonshi ba,hannunshi taji akan fuskarta yana shafar kumatunta ahankali ta lumshe idonta sakamakon jin bakinshi bisa nata,sakinta yayi dakyar ta fice ta shiga gida.
Tunda ta shiga gida takasa daina tunanin lamido da abinda yayi mata kasa bacci tayi sai juyi take tana aikin tunaninshi dakyar bacci barawo ya dauketa,shi kanshi lamidon shima hakace ta faru dashi domin shima ya kasa mancewa da yanayin da ya samu kanshi lokacin da yake tare da ikhlas.
Tunda haka ta faru tsakaninsu ikhlas take jin kunyarshi sam ta kasa hada ido dashi lamido ya ganeta sarai amma yayi biris da ita ya share ya nuna kamar bai fahimci abinda take nufiba alhalin ya gane domin ko magana yake mata bata taba daga ido ta kalleshi sai dai ta sunkuyar da kanta kasa gashi sai tayita kakkawar da kanta dan kar su hada ido,dariya al'amarin ikhlas yake bashi sai dai hakan yana burgeshi domin kunyar ikhlas ta dace da ita kuma tana yi mata kyau saboda ita kunya awurin mace ado ce.
Kwana biyu da faruwar wannan lamari inna ta shirya tatafi jimeta bikin yar yarta da ikhlas tayi niyyar tafiya amma lamido ya hana saboda lokacin sadiq bashida lafiya yana zazzabi,
Ikhlas na zaune takaicin duniya ya isheta lamido ya shigo shida sadiq,
"Wai damuwar me kike yi? Saboda inna bata nan? Kawai kibari zan zo na tayaki kwana" yafada cikeda tsokana yana dan kasalallen murmushi wanda ya kawata fuskarsa, bata kulashi ba ta dauki sadiq shikuma lamido ya fice,
Karfe 9 ta gama shirinta ta kwanta itada sadiq bayan tayi masa shirin bacci, har ta dan fara bacci taji shigowar lamido,tsayawa yayi yana kallonta ita da sadiq din, tana sanye cikin riga da wando dark blue masu tambarin fari ajiki amma rigar mai budadden kirji ce mai dan siririn hannu,
Abayanta yaje ya kwanta ahankali ya rungumeta ta baya,
"Abban sadiq baka tafi gida ba?" Ta tambayeshi domin ita bata zaci abinda yafada dazu cewar gaske ne ba,
"Yau zan tayaki kwana ne" ya mayar mata da amsa yana shakar ni'imtaccen kamshin dake tashi daga jikinta domin wani irin kamshine wanda gaba daya ya kasa gane kalar kamshin da jikinta yake fitarwa,shi kanshi shi dinma wani kayataccen kamshi ne mai dadin gaske yake fita daga jikinsa yana ratsa hancin ikhlas,
"Na yafe ka tafi wurin matanka" tafada tana lumshe idanuwanta,
Jiyo da ita yayi tana fuskantarshi wanda har tana iya jiyo saukar numfashinsa akan fuskarta,
"Duk basa nan sun tafi numan bikin kanwar fadila idan kuma baki son kwana dani ne sai naje na tafi na kwana ni kadai" yafada bayan yasaka hannuwanshi ya zagayeta ajikinshi,
Shiru tayi ta lumshe idanunta tana jin yanda ya shiga jikinta ya matseta duk motsin da zatayi ajikinsa ne bayan kuma ga fili nan da yawa abayanshi ya bari,
"Abban sadiq ka matseni fa" tace dashi ahankali,
Yana jinta ya rabu da ita daga karshe ya saka hannunshi jikinta yafara mika mata sakonni masu nauyin fada, cikin wani irin yanayi wanda bazai faduba suka shiga daga shi har ita wanda sun dade acikinsa kafin lamido ya iya barinta bacci mai dadi ya daukesu.
Can cikin dare yaji sadiq ya farka tashi yayi yaje ya daukeshi yabashi ruwa yasha ya maida shi ya kwantar ya koma jikin ikhlas ya kwanta,
Kiran asubar farko ta tashi tayi alwala tayi salla,lamido ta kalla wanda ke kwance yanata faman bacci,
Ganin 6 saura yasata zuwa ta fara tashinsa, juyi yayi ya bude Idonshi daya,
"Abban sadiq ka tashi kayi salla" ikhlas tace dashi ahankali idonta akasa, hannunta ya riko cikin nashi wanda har sai da taji wani irin yarr!,
Kamar meyin rada ya bude baki yace,
"Akwai ruwan zafine?"
Girgiza Kai tayi alamun babu, "to kije ki dafa min dan sai nayi wanka kafin nayi salla" yace da ita yana shafar hannunta da lallausan hannunshi,
"Wanka? Wanne irin wanka kuma?" Tafada ba tare data sani ba,
"Irin wankan da miji yake yi idan ya kwana a dakin matarshi" ya bata amsa bayan ya lumshe kyawawan sexy eyes dinshi.
WhatsApp: 08161892123
No comments:
Post a Comment