Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Thursday, 11 January 2018

RUWAN KASHE GOBARA! 58



_58_

Ahankali ta dago da kanta ta kalleshi,amma ta kasa magana saboda kunyar data gama rufeta wani irin nauyin lamido take ji marar misaltuwa amma takasa yarda da abinda yafada cewar yaga kirjinta, kanta ta sunkuyar cikeda kunya,
"Meya faru dazu kike yimin waya?" Tajiyo muryarshi yana sake yi mata magana,
"Am dama gidan ni'ima nake son zuwa zanje na dubo ta bata da lafiya"
"Yaushe?"
"Idan anjima"
"To ba yau ba"
Yana gama fadin haka ya fita daga cikin dakin, binshi tayi da kallo aranta tana jin mamakin wannan isar tashi lallai ta yarda maigida ko yaya yake akwai nuna iko,
Shiryawa tayi ta kwanta tunda ya hanata zuwa gidan ni'iman, tana nan akwance ta jiyoshi yana yiwa innah sallamar ya tafi, ko dakin nata bai dawoba ya wuce,
Innah ce ta shigo dakin nata ta karbi sadiq ta goyashi ta fita, wayarta ta dauka ta kira matar yayanta ta hadata da abdallah suka fara hira, kusan kullum katin wayarta yana karewa ne sanadiyyar hirarta da abdallah duk lokacin da tayi recharging to shi zata kira.
Misalin karfe uku na yamma tana daki tana yiwa sadiq wanka lamido ya shigo,dan satar kallonta yayi ya kalli yaronshi,
"Sadiq zaka rakani unguwa? Shirya maza ka rakani" yafada tareda ficewa,shirya Sadig tayi cikin blue din riga da wando fari ta saka masa farar safa da blue din takalmi, turare ta fesa masa,
Dagashi sama tayi tana dariya "zakaje wurin abba? Zaka raka abbanka unguwa ko? To zo na kaika abba"
Tana saukeshi taga lamido atsaye yana kallonta kur ko kiftawa ba yayi dan haka taji wata irin kunya ta kamata, mika masa sadiq tayi tana cike da jin kunya,
Karbarshi yayi "yawwa saddiqu na, kayi kyau my boy"
Har yakai bakin kofa yajiyo maganarta "iya sadiq ne zai yi rakiyar"
"Ehh" yabata amsa,
"Saboda me?"
"Saboda mata basa zuwa wurin"
"Akwai wurinda mata basa zuwa dama?"
"Da akwai"
"Inane?"
"Gidan kallon ball"
Dariya ta danyi yayinda shikuma lamido ya fice dauke da sadiq a kafadarsa.
Tunda suka fita gidan kallon ball yatafi shida bash basu baro wurin ba sai 9 lokacin har sadiq yayi bacci,
Ajiye bash yaje yayi a gida sannan ya nufi gidan innah,
Ikhlas na kwance ta zuba ido ta zuba ido amma shiru babu lamido babu alamarsa dan haka tayi shirin baccinta tayi kwanciyarta,
Har ta dan fara bacci sama sama taji shigowar lamido yana dauke da sadiq a kafadarshi yana bacci,
"Har kin fara bacci?"
"Abban sadiq sai yanzu?" Tafada tareda jan blanket ta rufe jikinta domin rigar bacci ne ajikinta kalarta pink marar duhu shara shara,
"Ehh shima har yayi bacci" kissing din sadiq yayi ya mika mata shi yana kallonta k'asa k'asa domin duk da cewa ta rufe rabin jikinta da bargo hakan bai hanashi hango kyakkyawar rigar baccin dake sanye ajikinta ba sannan ga yalwataccen gashin kanta nan mai mutukar shek'i da bak'i daure wuri guda kanta babu koda dan kwali,dakyar ya iya daurewa yayi controlling din kanshi ya daidaita nutsuwarshi ya dauke idonshi daga kanta ya juya ya fita,
Kwatar dashi tayi ajikinta ta koma ta kwanta tana tunanin al'amuran rayuwarta musamman ma mahaifinta wanda yayi watsi da rayuwarsu ita da yan uwanta domin rabonta dashi tun lokacin da ya koreta daga gidansa har yau bata sake jin labarinsa ba.
Washe gari da safe bayan ta shirya tsaf ta fita falo da sadig a hannunta, kan dining taje ta zubo ruwan zafi ta hada tea takoma falo ta zauna,
Zille zille sadiq yafara nan ta duka da niyyar ajiye cup din tea din amma cikin rashin sa'a sai sadiq ya shuri hannunta da kafarshi nan ruwan zafin ya zuba akafarshi,
Kuka ya cillara wanda har sai da innah ta fito daga dakinta tana tambayar meya sameshi,
Mikewa ikhlas tayi tana rike dashi,
"Wlhi innah konewa yayi da ruwan zafi"
"Konewa? A ina? Muga?"
Innah tafada agigice, karbarshi inna tayi ta duba kafar wacce tuni har wurin yayi ja ya tashi sosai,
"Wai wai haka wurin ya kumbura? Maza kira lamido yazo ya kaishi asibiti"
Agigice ikhlas ta dauko wayarta tafara kiranshi, yana kwance adakinshi shi kadai kasancewar yanzu ikhlas da fadila sun hade masa kai fushi suke dashi,
"Hello" yafada ahankali,
"Abban sadiq kazo ka kai sadiq asibiti"
"What" yafada da karfi tareda mikewa, ko wanka baiyi ba ya saka kaya ya fita.
Aguje yaje gidan yana yin packing ya fito a hanzarce ya shiga cikin gidan, afalo ya iske innah da ikhlas ga sadiq nan kuma a hannun innah sai tsaga kuka yake,
"Innah wai meya sameshi ne?" Yafada arude,
"Konewa yayi" innah ta bashi amsa,
"Konewa? Garin yaya"
"Tea ikhlas ta hada shine ya shureta da kafarsa tea din ya zuba a kafarsa"
Kamar wanda zai doketa haka yayi kanta yana yayyafa mata ruwan masifa,
"Wannan wanne irin sakaci ne? Ya za ayi ki dauko tea kuma ki ajiye akusa dashi, na fuskanci sam bakida kula akan yaron nan,you are very careless, yanzu ki duba kiga yanda yaron nan ya kone saboda tsabar sakacinki..."
Ikhlas ji tayi kamar ta fashe da kuka saboda tsabar takaici,
"Haba lamido ya zaka tisa yarinya agaba kayita yi mata fada haka.." Innah tafada tana kallonsa,
"Innah wallahi sakacinta ne.."
"Ba sakaci bane lamido domin babu wanda yafi uwa son danta, idan da ace tanada yanda zata yi da bata bar yaron nan ya kone ba da gara ita ruwan zafin ya konata, kabar wannan maganar ka karbeshi ka kaishi asibiti"
Bai kara magana ba ya karbeshi ya fita, wani chemist ya kaishi aka daye fatar aka yiwa wurin dressing da bandeji, jin kukan yaron yake kamar me,
Ita kam ikhlas tafiya lamido yayi yabarta da mamaki saboda yanda ya dage yake ta yi mata fada kamar zai daketa,
Ana gama yiwa sadiq dressing din ya daukeshi zuwa gidanshi, dakinsa ya wuce dashi ya kwantar dashi akan gado domin lokacin ya daina kukan,
Kayan jikinsa ya cire ya shiga wanka, yana bathroom yana wanka ihsan ta lek'o d'akin nan taga sadiq a kwance,
Tabe baki tayi ta juya tafita ta nufi dakin fadila,
"Kinga yau kuma abinda Nagani? Um yau ni naga sabon salo wai kiran salla da usir ko kin san wannan gayen d'an ikhlas yaje ya dauko yazo dashi cikin gidan nan?"
"Wai dagaske ko da wasa?" Fadila ta tambayeta,
"Wallahi dagaske, zama ki ganshi zo muje ki gani" jan hannun fadila ihsan tayi zuwa falo suka nemi wuri suka zauna suna jiran suga fitowar lamido.
Fitowa daga wankan lamido yayi ya shirya ya sa kaya yanayi yana yiwa sadiq wasa,farar t shirt mai dogon hannu ya saka da wando baki, turaren silver hummer ya feshe jikinsa dashi,
D'aukar sadiq yayi ya fita yana cewa sadiq "yarona ka gaji ko muje na kaika wurin momy" dorashi yayi akan kafad'arshi ya fita yana murmushi domin yana mutukar kaunar sadiq,
Su ihsan yagani afalo suna zaune kowacce ta dora daya akan daya fuska adaure ita kuwa fadila cingom take tauna ta turo dan kwalinta gaban goshi.

WhatsApp: 08161892123

No comments:

Post a Comment

Pages