Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee wadda sananniyar masoyiyar tsohon shugaban kasace, Janar Ibrahim Badamasi Babangida kuma a bayabayannan ta fara nuna goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar tayi wasu kalamai masu kaushi akan shugaba Buhari ta masoyanshi.
Ummi ta yi tambaya a dandalinta na sada zumunta da muhawara cewa idan ba atikuba wa kuke tunanin zai iya/ya kamata ya mulki Najeriya?, mutane sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan wannan tambaya ta Ummi.
Daga cikinsu akwai wani bawan Allah daya ce shi yana ganin Atiku baya daga cikin wadanda suka cancanci zama shuwagabannin Najeriya.
Ummi ta mayarwa da wannan mutumin amsa kamar haka"
kin Mutane da basa fahimtar turancin da bai taka kara ya karya ba, abunda nayi posting fa ba dogon magana nake so ba ko kushe wani dan takaran da ba naka ba. abunda post dina yake nufi shine, in Atiku ne dan takararka ka rubuta sunansa in kuma bashi bane ma ka rubuta sunan dan takaranka ko kuma ka rubuta nobody amma ba surutai na adawa nake so ba a comment pls dan in surutan adawa kuke so akan Buhari to ai in kuna da kunya baku da bakin magana domin a abubuwan da yayi alkawarin zaiwa kasa in an zabeshi har yanzu baiyi ko daya ba kuma duk wanda zaiji tsoron Allah ba tsoron Buharin ba yasan baiyiwa kasa komai ba in banda talauci da fatara da yunwa daya sa kasar a ciki ammah talaka da yake mahaukacine baisan ciwon kansa ba wai har yanzu shi yake so.
Mtwssss Allah ya sauwake da yan Nigeria hausawa.
Wallahi da a turaine bai isa yayi bakin milki irin wannan ba, da talakawan da kansu zasu ce a canja shi"
No comments:
Post a Comment