_42_
Sai da ya huta sannan ya fita shida bash zuwa kasuwa, kayan da zai bawa brother dinshi gifts yaje ya siyo,
Lokacin da ya dawo gida har ihsan da fadila sun tafi gidan bikin dan haka bedroom dinshi ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito domin zuwa wurin bikin amma kuma gabansa sai faduwa yake bai san dalili ba,
Farar shadda yasaka da jar hula, dinkin iya gwiwa ne rigar,yayi kyau sosai, komai nasa mai kyaune, motarshi ya dauka ya fita zuwa gidan innah lokacin karfe 4 na yamma,
Dakyar ya samu ya ga innah saboda jama'ar da suka cika gidan shikuwa baffa baya nan, dangi sai tsokanarshi suke "kaga mai mata biyu, da wuri zaka tsufa"
Dariya kawai yake yi yayi gaba, acan gate ya hango brother dinshi dan haka ya karasa gareshi suka rungume juna,
"Broz ina ne wurin walimar ne?"
"Mubarak hotel ne Lamido, kaje nima yanzun nan zanzo, kaga sai ku gaisa da yayar taka"
Murmushi Lamido yayi "congrats broz"
Juyawa yayi ya hau motarsa yafita ya nufi wurin walimar,
Lokacin da yaje anfara gudanar da wa'azi amma amarya da ango basu karaso ba, zama yayi awurin da aka warewa maza nan ya ciro phone dinshi yafara chtn, mintuna kadan yaji mai wa'azin yana shelar cewar ango da amarya sun karaso zasu shigo yanzu,
Daga dara daran manyan fararen idanuwanshi yayi ya soma kallonsu, tasha jan leshi da lifaya ja an nannade mata jikinta baka ganin komai ajikinta sai fuskarta wacce tasha kwalliyar amare,
Mikewa tsaye yayi yana kallonta, ahankali ya murza idonshi ya bude domin gani yake kamar mafarki yake yi,
"Pretty..." Yafada ahankali muryarsa tana rawa, sai binta yake da kallo daga karshe dai ya tabbatar itace saboda bazai taba mance kamanninta ba,
Wani jiri ne yafara daukarsa babu shiri yafita daga cikin hall din, wani juyawa yaji kanshi yana yi ga wani irin ciwo da ya dauka,
Ahankali ya shiga motarsa ya fizgeta zuwa gidansa, gudu ya sharara mintuna kadan ya isa gidan, dakinsa yawuce ya rufe kofa ya kwanta akan gado,
Hotonta ya janyo yafara gani kawai sai ya fashe da kuka kamar wani karamin yaro,
Kuka yake wiwi kamar tababbe,
"Shikenan na rasata, narasaki pretty, narasaki" yafada yana kuka,hotonta ya rungume akirjinsa yana kuka sosai,
Har mangaruba tayi su fadila suka dawo bai bude kofar ba yana ciki yana kuka, kasancewar ihsan ce dashi yasata zuwa ta fara nocking din kofar tashi amma bai budeba,
Sarawar da kansa keyi masa yasashi dole yin shiru yabar kukan, nan take zazzabi ya rufeshi babu dadewa baccin wahala yayi gaba dashi bashi ya farka ba sai tsakar dare misalin karfe 3 daidai,
Kansa ya rike wanda yake jinsa yayi masa nauyi sosai, dakyar ya iya mikewa yaje toilet yayi alwala yazo yayi salla, ko tantama baya yi yasan jininsa yahau karshen hawa,
Wani sabon kukan yafara, kwana yayi yana kuka ciwon kai kuwa kamar kansa zai tsinke da azaba, sai da gari ya waye ihsan tazo tana buga kofar sannan ya tashi ya bude,
Kallo tabishi dashi duk fuskarsa ta kumbura idonsa kuwa ba acewa komai saboda jan da yayi bau,
"My Lamido meya sameka?" Ta tambayeshi tana shafar fuskarshi,
Murmushin yake yayi "bani da lafiya ihsan gashi harda ciwon ido"
"Ayya sorry naga fuskarka ta dan kumbura gashi idonka yayi ja da yawa"
Bakin gado yakoma ya zauna ya tura hoton pretty kasan gado da kafarshi gudun kar ihsan tagani, kusa dashi tazo ta zauna ta kama hannunshi duk ta damu,
"My Lamido na kawo maka tea?"
"Kawo min dan kadan"
Tashi tayi tafita, ahankali ya goge kwallar idonshi shikam yasan dole ciwon zuciya ya kamashi domin bazai iya sanarwa da yayansa cewa wacce yakeso ya aura ba,
Ihsan ce ta shigo dauke da kayan breakfast akan farantin silver, tea ta hada masa yana daga kwance kafaufunshi akasa yana kallon sama,
Jikinshi ta shiga ya tashi tafara bashi, dakyar yasha rabin cup domin jin shayin yake kamar madaci yake sha,
Ganin ya dade baya nan yasan cewar ihsan tana da bukatar kasancewa dashi, ahaka ya daure duk da baya cikin nutsuwarsa ya kulata,
Wanka yaje yayi yafito ya shirya cikin kananan kaya farar t shirt da bakin wando, bakin glass yasa afuskarsa yafita ya nufi gidan innarsa domin ya yanke shawar cewar nanda kwana biyu zai tafi Kenya,
Lokacin da yaje yan biki duk sun tattafi saura guntu, kebewa sukayi da inna ya sanar da ita zai koma Kenya jibi,
"Lamido lafiyarka kuwa? Naga kamar baka da lafiya" innah tace dashi tana duban fuskarshi,
"Ehh innah, ciwon kai nake yi da ciwon ido yanzu ma idan nafita sai naje asibiti naga likita"
"Kai Lamido kullum kai kenan a ciwon ido anya kuwa?"
"Eh inna lalura ce ai"
"To Allah yabaka lafiya"
Tashi yayi yanufi side din baffa yana shiga ya samesu tareda yayanshi sadiq,
"Ah broz baka je kun gaisa da yayar taka ba" yayanshi yafada yana murmushi,
"Zanje ai broz banida lafiya ne"
"Allah ya baka lafiya"
Zama yayi suka gaisa da baffa anan Lamido yake sanar masa da jibi zai koma, tashi yayi ya fita yashiga motarsa yana driving yana kuka, tabbas yasan indai ya sanarwa da yayanshi cewar matarsa itace farin cikinsa itace burinsa to yasan zai bar masa to amma baya son yayi hakan saboda baya son ya zamo daga cikin mutane masu son kansu,
Abakin kasuwa yayi packing, hannunshi yaduba wurin da ya rubuta sunanta gashi nan radau rubutun yayi baki kamar irin zanen nan na tatu wanda turawa suke yi,
Idonshi ya lumshe wasu hawayen suka sake bin kumatunsa,
Wurin da ya yimata fyade yafara kallowa acikin zuciyarsa, karar wayarshi ce ta dameshi, ahankali ya zarota daga aljihunsa, bash ne dan haka ya daga yana share hawayen fuskarsa,
"Hello bash"
"On top kana inane?" Bash ya tambayeshi,
"Ina bakin kasuwa"
"To bari nazo"
Kashe wayar yayi ya kifa kansa ajikin sitiyarin motar yana kuka, har bash yazo bai saniba sai da ya shigo cikin motar ya dafashi, dagowa yayi fuskarsa jagaf da hawaye kamar karamin yaro.
No comments:
Post a Comment