Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Friday, 15 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 33



_33_

Yana fitowa daga dakinsa yaga mutane nan mata suka shiga yin guda suna tafi,
Bash ne ya rankayo yazo ya kama hannunshi yana murmushi,
"Kayi kyau on top"
"Nagode" yafada atakaice tuni masu hotuna da video coverage suka fara aikinsu na haska Lamido,
Mota yaje ya shiga kirar _Lexus_, bash yajasu suka rankaya domin tafiya kauyen Numan wanda canne tushen su fadila.
Misalin karfe 12:30 aka daura auren Lamido da fadila akan sadaki naira dubu hamsin, daga nan kuma cikin garin yola suka dawo unguwarsu ihsan wanda gidansu ke Sultan Road lokacin karfe 1:30 dan haka ana idar da sallar juma'ah a babban masallacin dake kofar gidan aka fara daura aure, ita dinma sadakinta naira dubu hamsin kamar na fadila, bayan daurin auren Lamido gida yakoma bash ya mayar dashi gashi amaren suna son ganinshi domin kowacce sai waya take yiwa bash tana tambayarsa ina angonta dole sai hakuri ya basu fadila kam harda kukanta domin kawayenta da suka yi secondary sch tare sun zazzo kuma sunata son su ganshi, ta wuri daya taji sanyi da bash yace mata da daddare akwai dinner kuma Lamido zai halarci dinner din yanzun ma dan bashida lafiyane yana zazzabi.
Lamido kam yana komawa gida daki ya shige yayi kwanciyarsa yanzu kallon kowa yake yi bashida bakin yin magana, wuni guda adaki yayishi har mangaruba tayi alokacin bash yazo domin ya shirya su tafi dinner, dakyar ya iya shawo kan lamido ya yarda ya shirya ya hade cikin purple din shadda gezna mai kyau yar gasken, bai saka babbar rigar ba iya yar cikin kawai yasaka yasa hula yarufe idanuwansa da bakin face,
Agidan baya ya zauna bash yajashi,
"Ina zamu fara zuwa?" Bash ya tambayeshi,
"Oho kai kasani"
"To gidansu fadila ya kamata mu fara zuwa domin itace uwar gida"
Lamido najinshi bai tanka masa ba, gidansu fadilan suka wuce wanda ke IBB road, suna zuwa bash ya kirata tafito, tasha kwalliya tayi kyau cikin wani pink din material,
Gidan baya bash ya bude mata kusada lamido, shiga tayi ta zauna, lamido ko juyawa ya kalleta baiyi ba,
"Lamido ya jikin tafada muryarta na rawa,
Juyawa yayi ya matso da ita jikinsa domin nesa dashi ta zauna yagane dalilinta nayin haka tsoro takeji kar ya yarfata,
Hannunwanta yakama acikin nashi,
"Da sauki fadila ya hidimar biki?"
Ba karamin dadi taji ba jin ya dan sakar mata fuska,
"Mun godewa Allah"
Hannunta ya murza acikin nashi yana kallon fuskarta babu laifi itama kyakkyawa ce wannan dalilinne ma yasashi yin soyayya da ita domin shi duk yan matanshi kyawawa ne,
"Kin san ku biyu na aura keda ihsan ko?" Ya tambayeta yana gyara mata gashinta da aka yanko mata gaban goshinta ya zubo,
Kai ta daga masa "ehh nasani"
"Yawwa to shikenan Allah ya zaunar daku lafiya"
"Amin" ta amsa tana lumshe idanuwanta domin wani farin cikine yake ratsata,
Gidansu ihsan sukaje suna zuwa itama tafito cikin kwalliya tasha material golden colour komai nata golden ta saka,
Itama bayan bash ya bude mata ta shiga ta zauna suka saka lamido a tsakiya, ganin fadila jingine jikin lamido hannunta cikin nashi yasata juyar da kanta,
"My Lamido ya jikinka"
Hannunta itama ya kamo ya rike cikin nashi,
"Da sauki my ihsan, ya taro?"
"Alhamdulillah my lamido"
Daga nan bai sake magana ba amma kuma yana lura dasu kowacce sai hararar yar uwarta take yi gashi sunki koda kallon junane,shikam da sun san abinda ke ransa da basuyi haka ba domin duk cikinsu babu zabinshi.
Har sukaje hall din da za agudanar da dinner din babu wacce ta kalli wata, shidai haka ya lallaba aka shiga wurin dinner din, wurin ya tsaru sosai yasha decoration gashi ya cika dam da al'umma
Wurin da aka tanadar musu suka wuce sukaje suka zazzauna kawayen amaren sai fulawa suke watsa musu da turare mai kamshi suna feshesu dashi.
Dinner din tahadu amma shi lamido sam babu fara'a akan fuskarsa har aka tashi anan kuma fada yaso barkewa tsakanin fadila da ihsan akan hanyarsu ta komawa gida,
Wata tsawa lamido ya daka musu "kai ya isheku kar Ku sake kuyi min fada"
Dolensu suka yi shiru, har akaje aka sauke ihsan basu kara magana ba, bai kulata ba tafita daga motar, haka itama fadilan lokacin da aka ajiyeta bai kulata ba, ita yasan gobe za akai masa ita gidansa ita kuma ihsan sai jibi wato ranar lahadi.
Suna zuwa gida ya fita daga cikin motar ya wuce bedroom dinsa, zama yayi ya dafe kansa wanda ke tsananin ciwo da sara masa kamar zai fita yabar jikinsa,
Wayarsa ya kunna tuni sakonnin abokanshi suka shiga shigowa rututu wanda duk na tayin murna ne, bai samu damar iya mayar musu da reply ba sakamakon sakonnin sunyi yawan da hakan bazata samuba.

No comments:

Post a Comment

Pages