_31_
Ita kanta fatar jikinsa ta sauya ta sake zama fresh yana tafe yana shakar iska yana fesarwa har ya karasa saukowa daga matattakalar jirgin,
Bash ya hango tsaye yana kallonsa yana dariya, inda yake ya karasa ya bashi hannu suka rungume juna,
"Welcome on top" bash yafada suka rungume juna suna dariya,
"Bash baka cika alkawari ba amma tunda gashi nadawo to zan dubo pretty na da kaina"
Dariya bash yayi aranshi yana cewa "maganar pretty kuma ai ta kare"
Amma afili sai yace "ok to shiga mota dai mu tafi kawai"
Bude motar sukayi suka shisshiga suka bar airport din,amma bash sai dariya yake yi kasa kasa ta mugunta wanda shi lamido bai fahimta ba domin bashida masaniyar auren da baffanshi zai yi masa gashi har mata biyu ris,
Suna tafe suna hira har suka karasa gidansu lamido anan yaga gidan nasu yasha sabon fenti an sake gyarashi tsaf, amma sai bai kawo komai ba aranshi,
Yana shiga cikin gidan innarsa ta tareshi da murna amma baffanshi baya nan bai dawo ba, babu kunya yatafi yaje ya rungume innah amma ita duk kunya ta kamata duk da kasancewarshi dan auta akwai alkunya irin nasu na fulani,
Jan hannun bash yayi suka karasa cikin falo duk ma'aikatan gidan sai sannu da zuwa suke yi masa,kujera yasamu ya zauna yana murmushi,
"Innah komai na gidan nan ya sauya yazama sabo badai duk murnar zuwana ne yasa akayi haka ba"
"Murnar zuwanka ne mana autan Baffa" inna ta bashi amsa,
Abinci aka gabatar masa kala kala nan ya zauna ya kwashi girki shida bash suna ci suna hira har Baffa ya dawo, rungumeshi Lamido yaje yayi yana murna domin rabonsa dasu tun lokacin da ya tafi Kenya sai dai agaisa awaya.
Har dare suna tare da Baffa da Lamido sunata hira, misalin karfe 9 suna falon Baffa azaune baffa ya kalleshi yana murmushi yace,
"Lamido ka shirya karshen satin nan zan daura maka aure da yaran da kake zuwa wurinsu kafin ka tafi Kenya fadila da ihsan ina nufin ranar juma'a mai zuwa kaga saura kwana biyu kenan"
Wani irin abune ya tasowa Lamido ya gilma ta idanuwansa tuni ya daina gani yaga duhu ya mamaye fuskarsa,
"Baffa aure? Kuma aurenma har mata biyu?" Yafada muryarsa na rawa,
"Eh Lamido abinda nake so dakai kawai kayi biyayya"
Shiru Lamido yayi bai sake magana ba har baffa da innah suka gama yi masa yan nasihohin da zasu yi masa ya tashi ya nufi dakinsa,
Rigar jikinsa kawai ya cire yafada gado yafara juyi yama rasa abinda zaiyi sai kawai yafashe da kuka, shi dai babban burinsa arayuwa yanzu shine yaga ya nemo prettyn shi ya aura yayi rayuwa da ita ashe hakan bazai faruba, kuka yake kamar ba namiji ba sai da ya raba dare yana kuka sannan ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa ya fito yazo ya kwanta, baccin da baiyi ba kenan, da safe kuwa tashi yayi da zazzabi gashi idanuwansa sunyi ja sun kumbura kamar wanda aka buga awurin.
No comments:
Post a Comment