_18_
Dukkaninsu sai da suka ga tashin jirginsu sannan suka nufi gida,
Lamido kam zama yayi jugum acikin jirgi yana raya abubuwa da dama acikin ranshi, hakika wannan tafiyar tashi ta yi sanadin da zaiyi nisa da wannan mahaukaciyar watikil kuma lokacin da zai dawo ba lallaine tana garin ba,domin bazai dawo ba sai nanda shekaru 3 ko 2,amma duk da haka dai zai ci gaba da tuntubar bash ko Allah zaisa adace, screen din wayarshi ya kalla anan take hotonta ya bayyana wanda aka zana,bakinshi yakai wayar yayi kissing din hoton gamida lumshe idanuwanshi.
*
Ikhlas sun jima suna hira itada asiya kafin su kwanta bacci wanda ita ikhlas sam bata samu runtsawa ba, kuka tafara marar sauti domin bata san inda zata dosa ba, domin sam bata son komawa gidan mahaifinta saboda dalilai masu tarin yawa amma ta yanke shawarar komawar koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar faruwar abubuwan da bata so.
Gyara kwanciyarta tayi tana share hawayen dake gudu akan fuskarta,
"Allah gani gareka kayi min maganin matsalolina" tafada acikin zuciyarta, yanda taga rana haka taga dare sam bata samu bacciba har gari ya waye.
Wanka tayi da ruwan dumi ta mayar da kayanta tasaka asiya ta gabatar musu da abin karyawa, Suna tsaka da cin abincin elmustapha ya shigo yana sanye da blue din shadda da hula,
Idonsa kur akan ikhlas yana kallonta shidai sam baya gajiya da kallonta domin kallon fuskarta yana sashi nishadi,
Zama yayi suka gaggaisa har ikhlas ta kammala tayiwa su asiya sallama, nan asiyan ta hadata da turarrurruka tarakota har kofar gida, ba karamin burgeta asiya tayi ba domin daga jiya zuwa yau ta fahimci macece me kirki.
Agaban motar elmustapha ta zauna tana kallon titi,
"Ikhlas wanne gari zamuje?"
Cikeda mamaki ta kalleshi,
"Zamuje ko zanje?",
"Za muje" yace da ita bayan ya hau titi,
"Kayi hakuri ka kaini tasha nashiga motar Zaria, wannan shine taimakon kadai da nake bukata daga gareka ahalin yanzu, sannan ina son ka rubuta min number wayarka domin zan runka kiranka muna gaisawa" ta karashe maganar tana goge hawayen idonta,
"Ikhlas hankalina yakasa kwanciya na nabarki ki tafi ke kadai, gashi kuma kin ki sanar dani wani abu game dake"
"Babu komai, ba wani abune yasani boye maka labarina ba sai don bana son bayyanashi ahalin yanzu amma kayi hakuri ai zumunci yanzu muka fara insha Allahu"
"To a Zaria awanne unguwa kike?"
"Kayi hakuri zan sanar dakai amma ba yanzu ba"
Shiru motar tayi babu wanda ya sake magana acikinsu har suka karasa tasha, da kansa ya fita ya samar mata motar da zataje Zaria ya biya kudin sannan yadawo inda take,
"Ikhlas Allah ya kiyaye hanya sannan dan Allah da zarar kin sauka ki kirani"
"Nagode madalla da irin taimakon da kayi min, Allah yasaka maka da alkairi, insha Allahu ina sauka zan kiraka koda kuwa a business center ne"
Wani kudin ya bata wanda zai kai kimanin dubu biyar, tana tafe tana hawaye har tashiga motar, bai bar tashar ba sai da yaga motarsu tabar cikin tashar, shi dinma kamar yayi kwallar yake ji domin yasan yagama shakuwa da ikhlas kuma yaso yaci gaba da zama da ita sai dai ina matsalar ni'ima tasha gaban zaman nasu,
Runtse idonsa yayi yana jin wani abu gameda ita, hakika tayi masa duk da cewar yasan koma daga ina ta fito to daga gidan arzikine domin surarta irin ta tsatson masu abin hannune, duk da haka ya kuduri niyyar bayyanar mata da soyayyarshi agareta ko Allah zaisa yadace.
Tagumi ikhlas tayi acikin motar sai zazzare ido takeyi domin rabonta da Zaria shekaru biyar kenan cif domin idan bata mantaba tun tana yar shekara 20 tabar gida cikin hali irin na tabin hankali,
Tunanin rayuwarta tashiga yi har suka karasa cikin Zaria,tana sauka daga motar ta nufi wani shago Wanda ake bayar da hayar waya,
Karba tayi takira elmustapha ta sanar masa da cewar ta sauka lafiya yanzu zata karasa gida,
Taxi ta shiga domin zuwa gidansu, tun ahanya tafara tambayar me taxi din ko yasan gidan ALHAJI AHMAD BUZU,
Nan da nan me taxi ya washe baki "haba hajiya waye bai san wannan mutumin ba acikin fadin garin nan, mutumin da yayi senata har na tsawon shekara takwas yanzu kuma ana cewa shi za abawa takarar gwamna ai dole yayi suna, can za akaiki?"
"Ehh" kawai tabashi amsa atakaice, titin Kaduna road ya dauka ya nufi wani hamshakin layi Wanda tun daga nesa suka fara hango jami'an tsaro suna kaiwa da komowa.
No comments:
Post a Comment