_15_
Cikin Sauri elmustapha yabi bayanta yana kiranta,
"Ikhlas, ikhlas karki tafi, ina zakije da wannan daren?"
Ko waiwayowa batayi ba har tafita daga gidan, baiyi kasa agwiwa ba yaci gaba da binta har yasamu ta tsaya,
"Ikhlas bai kamata ki biyewa maganar ni'ima ba, kin san halinku na mata babu wuya kun dauki kishi akan dan abinda bai kai ya kawo ba"
Murmushin karfin hali tayi ta kalleshi,
"Hakane amma kayi hakuri domin wlh nagama zama agidanka, nagode da irin taimakon daka bani alokacin da bani da wanda zai bani, ubangiji Allah ya saka maka da alkairi, zan tafi asalina zanje na nemi dangina domin kaima nabaka dama ka zauna da iyalinka lafiya"
"A'a ikhlas babu inda zakije zaki cigaba da zama tare damu"
Girgiza kai tayi "idan naci gaba da zama agidanka ina haifar maka da matsala kaida iyalinka banyi maka adalci ba sannan na mayar da alherin da kayi min da sharri, bai kamata nayi maka haka ba, yin haka zaisa mutane su kyamaci yin Alheri bayan kuma shi ALHERI DANK'O NE"
Dafe goshinsa yayi da hannunsa,
"Ikhlas kar ki tafi acikin daren nan bana son abinda yafaru dake abaya ya sake faruwa dake yanzu"
Shiru tayi tana kallonsa, "kiyi hakuri narakaki gidan abokina ki kwana, gobe da safe zanzo na kaiki tasha nasaki a motar da zata kaiki garinku"
Tuna alherin da yayi mata yasata kasa yi masa musu, gaba yawuce tabishi abaya har zuwa layin dake baya da gidansa,
Wani gida suka shiga wanda yake madaidaici kamar nasa, gidan abokinsa ne musbahu wanda shima lawyer ne me zaman kansa,
Sun tarar dashi tareda matarsa Asiya mace mai kirki da fara'a, cikin sakin fuska ta taresu,
Karya yayi musu cewar kanwar abokinsa ce zata wuce gida gobe daga sch take kuma gashi ni'ima bata nan shine ya kawota nan domin ta kwana,
Murna sosai Asiya da musbahu suka yi, nan yayi musu sallama ya tafi azuwan gobe da safe zaizo ya dauki ikhlas yakaita tashar motar da zata hau zuwa garinsu.
*
Har inna ta shigo cikin dakin yana kwance da zazzabin ajikinsa yana rawar dari,
"Kaico, Lamido wannan zazzabin naka wanne irine? Sai ya sakeka sai ya sake kamaka ko asibiti zakaje?"
Dakyar ya iya girgiza kanshi,
"A'a innah, bani magani kawai"
"Lamido dazu mafa saida nabaka maganin nan kasha gashi yanzu ya sake rufeka"
Kansa ya dafe yana haki "innah wannan zazzabin wlhi mai zafine, har cikin kashina nake jin zafinshi, washh, wayyo Allah na"
Matsawa tayi kusa dashi "sannu to daina kuka kar kanka yayi ciwo"
Tashi zaune yayi "innah bani ruwan zafi nayi alwala banyi salla ba"
Bathroom dinta ta shiga ta tarar masa ruwan zafi ta ajiye masa ta dawo inda yake zaune yana rawar dari,
To taso kayi alwalar maza, tashi yayi yabi ta gefenta ya shige bathroom din yayi alwala ya fito, salla yayi yana daga zaune, yana idarwa ya sake tukunkuna ya kwanta.
Sai da ya kwashe kwanaki 8 yana wannan zazzabin,aranar da yaji ya dan samu sauki yafita yawon neman wannan mahaukaciyar ko Allah zaisa ya dace amma shuru bai ga alamunta ba,
Wurinda ya sameta har yayi mata fyade ya nufa anan ya iske mutane kowa yana hada hadarsa ta siye da sayarwa,shago mai lamba 2 ya shiga, kamar Wanda zai sai wani abu yafara dube duben kayan dake jere akan kanta,
"Malam me kake so?" Mai shagon ya tambayeshi,
Sumar kanshi ya shafa,
"Ina neman turare ne explore"
"Bamu dashi sai dai ka duba wasu"
"Ok bani nagani"
Turaren aka shiga jido masa yana dubawa yana tambayar kudinsu,
"Uhm bawan Allah nikuwa da ina ganin wata mahaukaciya amma yanzu kwana biyu narabu da ganinta"
"Ayya ai wannan yarinyar rabonta da nan anjima ina jin wani gun tayi ko kuma saceta akayi kasan mutane da rashin tausayi"
Iya kaduwa Lamido ya kadu da jin kalaman wannan mai shagon dandanan yaji hankalinsa ya tashi nutsuwarsa ta goshe yayinda bacin rai ya ziyarceshi, batare da yakara cewa komai ba ya zabi turarurrukan guda uku yabiya kudin yafita, motarsa ya shiga amma kuma yakasa tukin zama yayi kawai jugum yana tunata hakika bazai taba iya mance kamanninta ba duk da cewar acikin duhun dare yaganta amma duk da haka yana ganin hotonta radau acikin zuciyarshi.
No comments:
Post a Comment