_63_
Yana zaune yana kallonta ta gama yiwa sadiq wanka ta shiryashi cikin jar riga da bakin wando ta fesa masa turare ta nufi wurin lamido dashi tana cewa,
"Zakaje ka gaida abba? In kaika wurin abbanka ko..?"
Mikawa lamido shi tayi wanda ke kwance akan doguwar kujera amma da alama ba kalau ba domin taga jikinshi yayi la'asar sannan duk girman idanuwanshi yanzu sun dawo kanana gashi sunyi wata kala,
Karbar sadiq yayi gamida riko hannunta, "yaushe zaki tare ne?"
Kallonshi tayi da mamaki "tarewa kuma? Basu innah sunce sai nan da watanni ukuba?"
Murmushi yayi wanda bai shirya yinshi ba, "gaskiya bazan iyaba, bazan jure ba, kifara shiryawa nanda sati biyu zaki tare"
Dagowa tayi ta kalleshi amma yanayin data ganshi aciki ya tabbatar mata cewar da gaske yake abinda yafa babu alamun wasa,
"Abban sadiq kabari mu kara koda wata dayane saboda kaga sadiq har yanzu.."
"Har yanzu me?" Sassauta muryarsa yayi yasake matse hannunta cikin nashi,
"Kina sone in mutu ko me?? Wallahi ina bukatarki akusa dani, i need you...! Yau dinnan zanje na samu baffa na fada masa, sassauci daya zan iya yi miki shine zan baki nan da sati uku kigama shirinki sai ki tare"
Yana gama fadin haka ya saki hannunta ya mike zaune yana rikeda sadiq a jikinshi,
Tsugunnawa tayi ta hada masa tea ta mika masa sannan ta ajiye masa sauran kayan agabanshi, tashi tayi ta shiga daki tana mamakin lamido saboda ita aganinta tunda yanada mata har guda biyu ai bazai wani damu da batun tarewarta ba,
Dakin tabi ta gyara ta fesa room freshener,tana kokarin fita lamido ya shigo,
"Hada min ruwa zanyi wanka" yace da ita ahankali,
"To" ta fada gamida juyawa ta shiga cikin bathroom din ta zuba mishi ruwan wankan ta fito,.
Falo ta fita ta zauna tahada tea tana sha, tana nan zaune ya fito rikeda waya a makale a kunnenshi yana magana,
"Nan da karfe nawa zaku karaso..? Ok sai kunzo"
Katse wayar yayi ya juyo yana kallon ikhlas wacce itama shi take kallo domin adon da yayi ba karamin kyau yayi mishi ba sannan ya fito dashi mutuka,
"Innah ce tace sun taho sun ma kusa karasowa"
"To Allah ya kawosu lafiya" ta fadi ahankali, juyawa yayi zai fita tayi saurin tsayar dashi,
"Abban sadiq dama akwai maganar da nake son muyi dakai.."
Dawowa yayi ya zauna yana saurarenta,
"Ina jinki"
"Uhm dama akwai wata islamiyya a unguwarmu ta da,marigayi ya karbo min foam din makarantar yace zan fara zuwa idan na gama cikewa to kuma sai ya rasu kafin nakai ga kammala cike foam din.."
"Wacce irice makarantar?" Ya tambayeta,
"Islamiyya ce ta matan aure kullum ake zuwa karfe 2 ataso karfe hudu saboda diploma ce ta Arabic"
"To zaki shiga amma ba yanzu ba sai bayan kin tare tukunna" mikewa yayi ya fita daga falon nan tabi bayanshi da kallo.
Misalin karfe 12 narana innah ta karaso tun daga wannan lokacin kuma ikhlas bata ga lamido ba sai duk taji ta shiga damuwa, karfe 9 tagama shirin bacci ta kwanta amma ga mamakinta sai ta kasa baccin domin kewar mijinta itace ta fara addabarta, juyi tayi ta rungume sadiq tana shakar kamshin turaren da lamido ya bar mata akan pillownta,
Tashi tayi taje ta bude drewar din kayanta ta dauko kayan baccinshi wanda ya kwana dasu adaren jiya,
Rungume kayan tayi tana jin kamar zatayi kuka, lallai rashin masoyi abune mai nauyin gaske domin ita sai yau ta tabbatar da hakan,
Kayan ta saka akan fuskarta tana shakar kamshin da suke fitarwa, ahankali ta mika hannunta kan bedside drewar dinta ta dauko wayarta, sakon text massage take son tura masa amma kuma ta rasa wacce kalma zata yi amfani da ita wurin bayyanar masa da irin yanda tayi rashinsa a wannan daren,
Daurewa tayi ta rubuta _I miss you abban sadiq_ ta tura masa, yana kofar falon gidan yana kokarin shigowa yaga sakon nata, murmushi yayi yasaka kai ya shiga,
Ahankali ya kama kofar dakin nata ya bude ya shiga ya lalubi makunnar wutar dakin ya kunna,
Duk wannan hidimar bata san yanayi ba domin idonta arufe yake ta lullube fuskarta da kayan baccinshi,
"Allah sarki my pretty ashe kema zakiyi missing dina adaren yau kamar yadda nima na tabbatar da zanyi missing dinki" yafadi hakan acikin ranshi,
Ahankali ya karasa kan gadon ta bayanta ya zauna ya dafata ya mika fuskarshi saitin tata, hannunshi yasa ya fara zare kayan baccin nashi wanda ta rufe fuskarta dasu,
Tsorata tayi ta zabura zata mike, cikin sauri ya dakatar da ita,
"Ina zakije? Nine fa" taji muryarshi yana yi mata magana, take ta dawo cikin hayyacinta sai kuma kunya tafara shigarta domin yazo ya kamata tana lullube da kayanshi,
"Meyasa kike da zurfin ciki? Meyasa kike son cutar da kanki? Ni nasan kinada bukatata kamar yadda nake bukatarki dan haka ki yarda ki tare lokaci kusa.."
Shiru tayi ta kasa koda motsi, juyawa yayi da ita zuwa kan jikinshi, "bakice komai ba"
Nan dinma shirun tayi masa, "uhmmm" ya sake fada ahankali, sanin ba zata iya yi masa magana ba saboda tana jin kunya yasashi rabuwa da ita ya dagota zuwa jikinshi ya rungumeta, wani irin sanyi yaji yana ratsa zuciyarshi, bakinta taji ya fara laluba da nashi,
Sun dade cikin wani irin yanayi kafin lamido ya kwantar da ita ya rada mata a kunneta "natafi sai da safe"
Bata iya bashi amsaba har ya tashi ya fita daga cikin dakin bayan ya kashe mata hasken dakin, juyawa tayi ta sake rungume kayan baccinshi tana murmushi da tunaninshi ta samu tayi bacci marar dadi domin sam bata ji dadinshi ba.
Washe gari lokacin da lamido yazo gidan wurin baffa yaje yace masa yana son ikhlas ta tare nanda sati uku, nan innah ta tada fada tace ba yanzu ba domin har yanzu sadiq bai gama yin kwariba dan haka ya bari sai nan da watanni uku kamar yadda akayi yarjejeniya dashi.Tashi yayi ya fita ranshi a bace ko cikin gidan bai shiga ba,
Tun daga ranar ya fara zarya agidan domin kusan kullum sai yaje gidan fiyeda sau hudu wani lokacin kuma har karfe 11 nadare yake kaiwa ganin abin yana neman yayi yawa yasa baffa kiran ikhlas yace tafara duk wani shiri wanda zatayi domin nanda sati uku zata tare agidanta,
Ba karamin murna lamido yayiba nan rawar kai ya karu kamar zaiyi me dan murna wanda har sai da su ihsan da fadila suka ji takaici, bash kuwa tsokanarshi ya shiga yi yana cewa shida yake da mata biyu kyawawa agida duk yanmata meye nashi na zumudi akan bazawara, duka lamido ya kaiwa bash yace,
"Bash baka san wacece ikhlas ba shiyasa, abin sirrine ba zaka ganeba"
Dariya bash yayi "wannan haka yake on top".
Gidan baffa sukaje bash yayi dropping dinshi ya wuce, cikin gidan ya shiga ya iske ikhlas a falo tana goye da sadiq yana bacci anan ta sanar masa cewar tana son zuwa Maiduguri kafin ta tare, da kyar ya yarda ya barta, dan haka ranar talata da safe ta shirya ta tafi amma ba ita ta isa gidaba sai daf da sallar magrib,
Tun da taje aka fara yi mata gyaran jiki irin na amare da sauran gyare gyare wadanda baza arasa ba, lokacin da taga abdalla sai da tayi mamaki domin ba karamin girma yayiba gashi kuma yana yi mata kama da wani Wanda ta kasa gane ko waye,
"Abdallah ka dada zama saurayi" tafadi tana dariya,
"Anty zaki tafi ki bar mana sadiq ko?" Abdallah yafadi yana murmushin da har sai da kumatunsa suka lotsa,ras ikhlas taji gabanta ya harba amma kuma ta gagara tuno wanda abdallah yake yi mata kama dashi,
"A'a abdallah bazan bar muku sadiq ba sai dai kai kazo mu tafi dakai"
Makale kafada yayi yace "ni bazanje ba awurin uncle Hussain zan zauna"
"Kaji ja'iri to dakai zasu tafi" ammi ta fadi tana dariya, sallamar yaya Hussain ce ta katse musu hirarsu,
Zama sukayi suka gaisa anan yake sanarwa da ikhlas cewa yabawa farida matarsa kudi wanda suka hada shida hassan gobe suje kasuwa itada farida su siyo duk abubuwan da take bukata domin tsofaffin kayanta kwasosu za ayi akawowa ammi itama tasaka adakinta, godiya sosai ikhlas tayi washe gari sukaje kasuwa itada farida nan suka fara jidar kaya masu tsada da kyau wanda ita dai ikhlas tsayawa kawai tayi tana kallon farida domin duk abinda ta nuna tana so daukoshi farida take ta biya kudin, bata san adadin yawan kudin da su Hussain suka bayar ba,
Sai yamma lis suka koma gida lokacin sun kammala siyayyar sun siyo dukkan abinda ya kamata, cigaba da gyaran jikin ikhlas akayi har ya rage saura kwana uku ta tafi yola wanda aranar da ta koma awashegarin ranar zata tare,
"Ina son kwalliya ciki harda irin wannan zanen da kuke yi a hannu da kafa.." Maganar lamido ce ta dawo cikin kunnuwanta hakan ta sata zuwa aka yaryada mata jan kunshi mai hadida baki wanda ya kama atafin hannunta da tafin kafarta radau,
Turaren wuta dana jiki da humra masu kamshin gaske aka harhada mata bayaga su kwalacca da sauran kayan kamshi,batun lamido kuwa tun ranar data bar yola yake faman kiranta awaya, kowanne lokaci cikin yi mata waya yake har ranar da zata dawo.
Tun asuba suka fita itada hajiya da matan yayunta ga kuma motar kayanta wanda yayunta suka sake mata, suna zuwa gidanta suka wuce dasu da motar kayanta bayan sun sauketa a gidan baffa, bata dade da sauka ba ta fita ta tafi saloon lokacin data dawo ta samu ni'iman elmustapha tazo gidan tana jiranta, yan kafi kuwa sai dare suka dawo bayan sun shirya mata dakinta da falonta tsaf, kitchen ne dai guda dayane ahade wanda nasune su duka ukun amma kowacce ta shirya kayanta agefe daya,sannan tunda sukaje gidan gaisuwa ce kadai ta hadasu dasu fadila da ihsan daga wannan kowacce shigewa dakinta tayi taki fitowa har suka gama jeren,
Adaren sukaje tsohon gidanta suka tattaro mata duk wani abu wanda zata bukata sauran kuma aka loda a mota domin tafiya dashi maiduguri,lokacin da suka je gidan saida ikhlas tayi kuka saboda tunowa da marigayi da tayi,
Sai wurin karfe 12 sannan suka samu damar yin shirin bacci,
"Kai mutuniyata kinga dakinki kuwa?? Komai ya hadu wallahi sannan ke din kanki ma kinyi kyau sosai, wallahi ina jin idan lamido ya ganki zaucewa zaiyi" farida tace da ikhlas tana dariya,
"Ai ni idanma akwai abinda yafi zaucewa zanso lamido yayi indai akaina ne" ikhlas ta fada acikin zuciyarta, amma afili cewa tayi,
"Dagaske? Bani labarin gidan dan Allah"
Kwanciya farida tayi tana cewa "kibari gobe idan kinje zaki gani ni yanzu ki kyaleni bacci zanyi domin nagaji"
Kwanciyar itama ikhlas tayi fuskarta dauke fa murmushi tana tunanin gobe iyanzu tasan tana tare da lamido a kusa da ita.
WhatsApp: 08161892123
No comments:
Post a Comment